Header Ads Widget

Nigeria@62: Ganduje ya hori Yan' siyasa suyi yakin neman zabe cikin lumana

Gwamna Abdullahi Ganduje

Daga: Salisu K Ismail

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya roki yan siyasa dasu kasance masu jurewa hamayya tsakanin su yayin da aka fara hada hadar yakin neman zabukan shekara ta 2023.

Ganduje ya bada wannan shawarar ne a Asabar din nan, yayin da yake jawabi wajen bikin cikar Nigeria shekara 62 da samun yancin kai, wanda aka gudanar a Asabar din nan, a filin wasanni na Sani Abacha Stadium dake kano.

Kamar ko wacce shekara bisa al'ada, cikin gudanar da bikin murnar zagayowar ranar samun yancin kan na kasa, hukumomin tsaro da kungiyoyin sakai na tsaro da Daliban makarantun sakandire sun gudanar da fareti (parade) na musannan a gaban Gwamna Ganduje, bayan da daga bisani kuma Gwamnan ya karanta jawabin sa kai tsaye ga jama'ar Kano.

Jawabin Gwamnan a wannan karon ya kasance shine na karshe a iya zamansa Gwamna, sakamakon wa'adin mulkin sa zai kare kafin zagayowar ranar samun Yan'cin Kasa na shekarar badi.

Duba da yadda yan siyasa suka dukufa wajen yakin neman zabe a yanzu haka, Gwamna Ganduje cikin jawabin nasa, ya roki Yan siyasa dasu kasance masu martaba junan su, ta hanyar juriya da juna da kuma gudanar da zakin neman zabe ba tare da muzgunawa juna da tada hargitsi ba.

A irin wannan lokaci da muke murna da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka, akwai bukatar daukacin Yan Nigeria a koda yaushe su dinga sabunta yarda da kasancewar Nigeria a matsayin dunkulalliyar kasa guda daya da zamu dawwama muna alfahari da ita," inji Gwamna Ganduje.

Haka kuma, Ganduje yace, nan gaba kadan, kafin ya mika mulki ga sabuwar gwamnati, zai kaddamar da dukkkanin ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar wadanda aka kammala su, kama daga aikin samar da wutar lantarki mai zaman kanta mallakin jihar Kano (IPP) dake Tiga wanda zai samarda megawatts 7.5 da Gadar sama ta Hotoro da Cibiyar kula da masu cutar daji (Cancer Center) dake Giginyu da sauran su.

Post a Comment

0 Comments