By Faruq Muhammad, Kano
Dan takarar majalissar tarayya a kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jam'iyyar NNPP Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya gwanjage mutanen yankinsa da jar da tallafin kudade domin bunkasa cigaban tattalin arziki da sauran al'amuran yau da kullum a yankin.
Yayin raban tallafin kudaden wanda ya gudana a Asabar din data gabata a garin Kofa, wasu daga cikin wadan da suka rabauta da tallafin sun samu zunzutun kudi a dunkule da suka kai N200,000, wasu kuma suka samu N100,000, Yayin da wasu kuma suka karbi tallafin N50,000.
Haka kuma, cikin wadan da suka samu tallafin kudin na Jarman Bebeji domin yin jari, akwai wadan da aka baiwa N50,000, wasu kuma N20,000 da masu N10,000 da kuma wadan da suka rabauta da N5,000.
Mutanen da suka amfana da wannan jari da tallafi sun hada da wakilan akwatuna, Shugabanni wato (Excos) a matakin karamar hukuma da mazabu na Jam'iyyar NNPP da PDP na Kiru/Bebeji da kungiyoyin mata da matasa na Kiru/Bebeji.
Dagatan Kiru/Bebeji da Limaman Juma'a da Malaman Kwankwasiyya da kungiyoyin Dalibai da Yan Social Media da Mafarauta da Yan Achaba da Mahauta da kuma masu bukata ta musamman na cikin wadan da suka samu rabauta da tallafin.
Taron ya sami halartar yan takarkaru na Kiru/Bebeji, manyan jagorori tare da shuwagabannin jam'iyyar NNPP/PDP na Kiru/Bebeji wadan da suka yi canjin sheka daga PDP zuwa Jam'iyyar ta NNPP.
0 Comments