By Faruk Muhammad
Ƙungiyoyin farar hula a Edo sun hau kan titunan Benin, babban birnin jihar, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.
Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna suna yin Allah-wadai da karin da kuma tsadar rayuwa a Najeriya.
Masu zanga-zangar dai sun ce abin na ci musu tuwo a kwarya inda suka soki matakin karin farashin man fetur yayin da ake fama da tsantsar talauci.
Masu zanga-zangar na dauke ne da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira 8,000 da Gwamnatin Tarayya ke yi shirin yi bayan cire tallafin man fetur ɗin.
Zanga-zangar ta zo ne makonni bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an cire tallafin mai. Tun bayan nan kuma farashin kaya da man fetur suke hauhawa a fadin kasar.
Yayin da gwamnatin tarayya ke cewa matakin an dauka ne don ci gaban kasa, masu suka na ganin zai jefa kasar cikin mawuyacin hali.
A ci gaba da daukar wannan mataki, gwamnatin tarayya ta bayar da shawarar bayar da tallafin Naira 8,000 ga ‘yan Najeriya amma daga baya ta ce za ta sake duba lamarin bayan sukar da shirin ya sha.
Gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya su yi hakuri kuma ta ce ana daukar matakan rage radadin cire tallafin.
...BBC Hausa
0 Comments