Daga Saidu Ahmad Dukawa
SHIMFIDA
A yayin da hankalin mafi yawan ‘yan Najeriya yake kan maganar nadenaden Ministoci da sauran mukaman siyasa, da kuma maganar tsadar da rayuwa ta yi, wata babbar masifar tana tinkaro kasar da ma yankin Sahel (Africa ta yamma da makwabtanta) baki daya.
Wannan masifar itace ta kokarin da wasu suke yi na hada fada tsakanin Najeriya (da sunan ECOWAS) da Kasar Nijer.
Tun lokacin da sojaji suka hambarar da gwamnatin farar hula a Nijer, America da Kasashen Turai suke ta shige da fuce suna ganawa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ta hanyar waya, da zuwa da kai, da gayyatarsa.
Abubuwa sai faruwa suke yi a guje a guje:
-Shugaba Tinubu ya bi sahun Shugabannin Duniya wajen yin Allah wadarai da juyin mulkin
-Ya kira taron gaggawa na kungiyar ECOWAS
-Ya fitar da sanarwa da sunan kungiyar na cewar lallai a dawo da hambararren shugaban kasar Nijer a lokacin da bai wuce mako guda ba
-Ya yi barazanar daukar matakin soji idan sojojin Nijer ba su dauki maganarsa ba
-Ya tura jakadu zuwa Nijer su tattauna da wadanda mulki yake hanunsu
-Najeriya ta katsewa Nijer wutarlantarkin da aka yarjajjeniyar kada su yi dam a jikin kogin Naija, don kada kogin ya kafe wutar Najeriya ta kayinji ta samu tasgaro;a madadin haka Najeriya ta yi alkawarin baiwa Nijer wutar lantarki
-Nijer ta sanar da ‘yanke alakar jakadanci da Najeriya, tun kafin a ji me jakadun Najeriya suka tattauna da shugabannin Nijer
-Idan ba a Ankara ba, sai ace masu mulkin a Nijer ba su ji maganar jakadun Najeriya ba, kafin a farga sai a ji Najeriya ta farma Nijer da yaki (Allah ya kiyaye!)
Tare da cewar jakadun da aka tura tsofaffin sojoji ne wadanda suka shahara wajen neman zaman lafiya, babu yadda za a yi su bada shawarar a yi yaki.
MATSALAR YAKI
Abin gudu game da yaki tsakanin Najeriya da Nijer yana da yawa:
-Yakin zai gurgunta harkokin kasuwanci da tattalin arziki
-Zai dada tabarbarewar harkokin tsaro a kasashen biyu, da Karin matsalar ‘yan gudun hijira
-Zai janyo a farmawa duk abinda ake jin haushinsa a Najeriya ace Nijer ce, a farmarwa na Nijer ace Najeriya ce (kamar matatun mai, da gonaki, da tsangayu)
-Za ta yiwu Nijer ta samu goyon bayan Russia da taimakonta, Najeriya kuma ta gaza samun goyon bayan America saboda Majalisar America da wahala ta sahalewa gwamnati taimakon Najeriya.
-Zai dasa gaba ta tsawon lokaci a tsakanin kasashen biyu.
Don haka wajibi ne a dukufa wajen hana wannan yakin, manyanmu da kanana kowa ya tashi tsaye.
ME NENE ABIN YI?
Izuwa yanzu ya kamata ace:
1.Kungiyar gwamnonin Arewa sun yi taro na musamman domin duba na tsanaki da fitar da matsaya ta ba su yadda da yaki ba
2.‘Yan Majalisar kasa ya kamata su yi zama na musamman akan maganar, su yi gargadi cewar ba za su sahalewa gwamnati shiga yaki ba
3.Sarakunan Arewa su yi taro na musamman su fitar da matsayar rashin goyon bayan yaki
4.Kungiyoyin al’umma daban daban su fitar da matsayar rashin goyon baya
5.Malamai da Limamai su magantu a majalisan karantarwa, da mimbarori, da shafukansu na social media
6.Kafafen yada labarai su yi kwarmato mai yawa na rashin goyon bayan yaki
7.Matasa ‘yan social media su yi hashtags na kin jinin yaki.
8.Kafatanin al’umma su dukufa wajen addu’a da istigfari da rokon Allah ya kiyaye yaki tsakanin Najeriya da Nijer ko yankin sahel baki daya.
KAMMALAWA
Gwammanatin Najeriya da gwamnatocin kasashen ECOWAS su guji tsunduma yakin da ba zai samu goyon bayan al’ummunsu ba.
A madadin yaki su dauki dukkan matakai na diplomasiyya wajen neman bukatarsu ga mahukunta Nijer. Wannan shi zai basu goyon bayan al’ummunsu kuma ana fatan shi Allah zai yi farin ciki da shi kuma ya taimakesu a shugabsncinsu.
Wassalamu Alaikum wa rahmatullah.
Saidu Ahmad Dukawa
BUK
4/8/2023
0 Comments