Header Ads Widget

Ambaliyar Ruwa: Jami'an Gwamnatin Adamawa da Kwararru na ganawa dan lalubo mafuta

Wani sashin da ambaliyar ruwa ta shafa a Adamawa


By Aliyu Muhammad, Yola

A yayin da ake ci gaba da samun kwararar ruwa a gabar kogin Benue da ke ci gaba da yin barna a Adamawa, gwamnatin jihar ta yi wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki daga sassan gwamnati da masu gudanar da ayyukan jin kai. 

Makasudin taron shi ne don a samar da hanyoyin magance wannan matsalar. 

Wakilinmu ya ruwaito cewar Biyo bayan ambaliyar ruwa da ta rusa gidaje tare da raba mutane da dama da muhallansu rahotanni sun ce an kafa sansanoni 11 a kananan hukumomi hudu na Yola ta Arewa da Kudu da Lamurde da Demsa.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya yi magana ta bakin mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta ya ce a matsayinsu na gwamnati, sun tashi tsaye wajen ganin an rage illar da ambaliyar ruwa ke yi wa al'umma.

Gwamnan ya nanata cewa ko da yake, an samu wasu makarantun da ambaliyar ruwan ta mamaye Amma hakan ba zai hana gwamnati yin shiri don ganin bai shafi ayyukan koyarwa ba. 

Tun da farko kwamishinan ma'aikatar dake kuwa da sake farfado da martabar jihar, Barrister Bello Hamman Diram da takwarorinsa na ma’aikatar yada labarai Neido Geoffrey da ta harkokin mata da ci gaban jama’a Wunfe Anthony sun ce taron ya zama dole domin kare rayuka da dukiyoyin Al'ummar jihar.

A cewarsu, samun dandazon Yan gudun hijirar da ba a taba ganin irinsa ba sanadiyyar ambaliyar ruwan ya zama abin damuwa, don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki su yi tunani da kuma duba yadda za a bi don tunkarar lamarin. 

Sun yi kira da a cigaba da wayar da kan jama’a kan illolin ambaliya, lura da cewa, a yayin da gwamnati ke yin nata bangaren wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya kamata ‘yan kasa su bada tasu gudunmawar ta hanyar daukar matakan kariya, kamar gujewa zama a bakin kogi, da yin gine-gine a hanyoyin ruwa.

Alkaluman da babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Adamawa Muhammed Suleiman ya bayar, ya nuna cewa magidanta 1,600 ne suka rasa matsugunansu, wadanda suka kunshi mutane 9,960 ke samun mafaka a sansanonin.

Post a Comment

0 Comments