Header Ads Widget

{Ra'ayi}: Rino Omokri Ya Kalubalanci Peter Obi Kan Wasu Muhimman Batutuwa Da Sukayi Kama Da Bangaranci

Mr. Rino Omokri


Rino Omokri Ya Kalubalanci Peter Obi Kan Wasu Muhimman Batutuwa Da Sukayi Kama Da Bangaranci.


Futaccen mai fashi baki kan al'amuran yau da kullun, Mr. Rino Omokri ya yi zazzafan kalubale ga tsohon Dan-takarar Shugaban kasa a tarayyar Nigeria a zaben 2023 karkashin tutar Jam'iyyar Labour Party Mr. Peter Obi kan wani abu da yayi kama da zargin nuna bangaranci da fiyaya nuna damuwa kan abubuwan dake faruwa tsakanin wani yanki zuwa wani yanki a kasar.

Rino Omokri ya zayyana zargin ne a sahihin shafinsa na Facebook, a ranar Talatar nan, 3 ga watan janairun sabuwar shekarar miladiyya ta 2024.

Yana mai cewa, cikin rubutun da yayi kamar haka;

"Babu wata ma'ana sosai akan maida hankali da Peter Obi yake game da kashe kashen dayake faruwa a jihar Filato bayan yana faruwa ne akowa ne sashe zuwa sashe, kashe kashen nan kusan duk iri daya ne da wanda akeyi a Kudu Maso Gabas da Arewa ta Tsakiya. 

Kudu maso Gabas shine yankin dayafi kowane yanki na Kudancin Najeriya rashin tsaro. Amma yaushe ka taba jin Peter Obi yana Allah wadai da kashe kashen dayake faruwa a Kudu maso  gabas kamar yadda yakeyi idan ya faru a yankinsa?

Ku fadi gaskiya. A shekarar 2022 kimanin mutane 449 aka kashe a Kudu maso Gabas, masu kisan basu wuce yan kungiyar Biyafira ba ko yan bindiga dadi. Sau nawa Peter Obi yayi Allah wadai da faruwar hakan? 

Ashekarar baya, wannan adadin ya ninku da kimanin kaso 12%. Amma mai Peter Obi yace? 

Sati shida daya wuce yan uwa su biyu, Chinedu da Omama an kone su kurmus agarin su Peter Obi, Onitsha. Yace wani abu game da faruwar hakan?

Lokacin da Peter Obi yake Gwamnan Jihar Anambra, darurukan mazaje ne akayiwa kisan gilla aka jefasu acikin kogin Ezu. Wane mataki Peter Obi ya dauka? 

Amma idan da hakan ta faru ne a jihohin Kaduna ko Filato, tuni Peter Obi zai garzaya acikin karamin jirgin da yayi karyar baya hawa irinsu, ya isa zuwa garin yana kukan karya.

Ko za'ace karya nakeyi? 2024 shekarar tona asirin makaryata ce!"
#GirgizaTeburi
Daga shafin Facebook na Rino Omokri

Post a Comment

0 Comments