Taron cika shekaru 33 da kammala karatu na kungiyar tsofaffin daliban kwalejin horon Malamai ta T/Wada Dankadai (TUDOBA 90)
From Editor Desk
Kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin horon Malamai ta Tudunwada Dankadai ta gudanar da babban taron ta na shekara-shekara karo na 33 tun bayan kammala Makarantar a 1990.
Da yake jawabi a lokacin taron, Shugaban Kungiyar, Dr. Hamza Muhammad Assani, yace ana gudanar da wannan taro ne a kowace shekara domin karfafa dankon zumunci a tsakanin 'yan kungiyar da tattauna nasarori da kuma kalubalen da aka fuskanta a cikin shekarar da ta gabata.
Dr. Hamza Muhd Assani wanda Malami ne a Jami'ar Sa'adatu Rimi dake nan Kano, ya yi bayanin cewa baya ga haka kungiyar ta kuma tsara manufofi akan yadda za ta cigaba da tallafawa tsohuwar Makarantar da kayan koya da koyarwa don tallafawa yunkurin gwamnati akan haka da kuma tallafawa iyalan 'yan kungiyar da suka riga mu gidan gaskiya.
Shugaban Kungiyar ya nuna jin dadin 'ya'yan kungiyar kan bayanin da ke kunshe cikin kunshin kasafin kudin gwamnatin jihar Kano na bana na gyara Makarantar baki dayanta a bana, inda ya jinjinawa gwamnati bisa wannan kudiri.
Dr. Hamza Assani ya kuma bukaci 'yan kungiyar su cigaba da rike zumuncin da ke tsakaninsu domin hakan a cewarsa zai taimakawa rayuwar 'yan kungiyar da 'ya'yansu da ita kanta tsohuwar Makarantar da suka kammala.
Haka zalika Shugaban Kungiyar ya taya wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar murna da suka sami daukaka a mukamai daban-daban na rayuwa wadanda suka hada da Sakataren Kungiyar Dr. Aminu Bala Danyaro na BUK wanda ya sami mukamin babban Mataimaki na musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Comrade Nura Haruna Rimingado Shugaban Kungiyar Ma'aikatan lafiya na Jihar Kano da Muhd Abdu Doguwa a matsayin DPM na Karamar Hukumar Tudunwada da Abdullahi Jinjiri a matsayin DPO na Birnin Kudu a jihar Jigawa.
Sauran da Kungiyar ta taya murna sun hada da Garba Haruna Dash na UN da Muazu Shariff Yako na Dangote Group of Companies Lagos da Musa Muhd Kibiya Assistan Comptroller Correctional Services da Usman Ibrahim Tudunwada da Ndidi Okoko da dai sauransu.
Taron ya sami halartar 'ya'yan kungiyar da dama musamman daga Jihohin Kano da Jigawa da kuma Kaduna.
0 Comments