Header Ads Widget

Gwamnati Kano cancanci yabo wajen fadada wuraren noman rani da samar da ruwan sha - Iliyasu Bagwai

Alhaji Iliyasu Wakili Bagwai


By Sha'aibu A Sani, Kano 

Tsohon Shugaban Kwamitin samar da ruwan sha na matatar ruwa ta Watari da ke Bagwai, Alh Iliyasu Wakili Bagwai ya yaba wa kokarin gwamnatin Jihar Kano na samar da ruwan famfo ba tare da katsewa ba a yankin Bagwai da kewaye. 

Alh Iliyasu Wakili Bagwai ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a yankin. 

Ya ce babu shakka gwamnatin Jihar Kano ta cancanci yabo a wannan bangare musamman yadda al'umar Bagwai da kewaye ke samun wadataccen ruwan famfo a koda yaushe duk da wannan yanayi da ake ciki na tsadar man Gas. 

Haka zalika tsohon Shugaban Kwamitin ruwan ya yi maraba da wani yunkurin gwamnatin Jihar tare da hadin gwiwar bankin bunkasa harkokin musulunci na duniya na fara aiwatar da aikin fadada wuraren noman rani da ke Bagwai da kewaye wanda ya kai hekta dubu daya. 

Ya ce wuraren da wannan aikin ya shafa sun hada da Bagwai da Dogon Dawa da Dullu da kuma Kauyen Adam a matsayin wuraren aikin noman rani na sashi na daya zuwa na 6.

Alh Iliyasu Wakili Bagwai ya Kara da cewa babu shakka idan aka kammala wannan aiki zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma da samar da abinci da ayyukan yi da kuma karuwar arziki a tsakanin al'umar yankin da ma Jihar Kano baki daya. 

Alh Iliyasu Wakili Bagwai wanda kuma tsohon ma'aikacin ma'aikatar noma ne, ya bukaci al'umar wannan yanki na Bagwai su yi amfani da wannan damar wajen dogaro da kansu ta hanyar kama sana'ar noma gadan-gadan musamman noman zamani da kuma baiwa gwamnati hadin kai a manufofinta domin inganta rayuwarsu.

Post a Comment

0 Comments