Daga Salisu K Ismail
Gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi ya bayar da umarnin biyan albashin dukkan ma'aikatan da su ka samu matsala wajen tantance su a manhajar IPPMS ta hanyar amfani da tsohon tsarin biyan albashi kamar yadda aka saba.
Idan za'a tuna, a baya kadan tin bayan hawansa karagar mulkin Jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya yi alwashin aiwatar da sabin tsare-tsare da nufin ingata tsarin aikin gwamnati da abinda ya shafi ma'aikatan ta yadda tsarin Jihar zai yi dai dai da zamani da kuma bunkasashi.
Sabanin yadda aka saba a baya wajen biyan albashi a 25 ga wata, Wasu daga cikin Ma'aikatan Jihar Jigawa dama na Kananan Hukumomin Jihar 27 sun fuskanci matsalar jinkirin samun albashin watan Afrilu sakamakon aikin tantance bayanan ma'aikatan da kuma maida bayanan nasu zuwa kan manhajar IPPMS da Gwamnatin ta bullo dashi wanda wani kanfani mai zaman kansa ke aiwatarwa.
Cikin sanarwar da maitaimakawa Gwamna na musamman kan Kafafan sadarwa na zamani Mallam Garba Al-Hadejawy ya futar a Larabar nan, ya yi karin haske da cewa, "Ma'ana; matsalar tantance wa, ba za ta shafi biyan albashin kowane ma'aikaci ba."
Sanarwar ta kara da cewa, "Za a ci gaba da biyan albashi, sannan ana yin dukkan gyare-gyaren da ya kamata wajen ganin an saka kowane ma'aikaci a cikin tsarin manhajar ba tare sa samun tasgaro a albashinsu ba."
Sanarwar Gwamnatin ta hannun Mai taimakawa Gwamna na musamman, Malam Garba Alhadejawy ya bayyana cewa, "An umarci ofishin ma'aikata na jiha (Office of the Head of Service) da ma'aikatar kuÉi ta jiha (Ministry of Finance) da zu zaĘulo dukkan ma'aikata masu matsalar tantance wa, da ma waÉanda ba a tantance ba domin a tantance su tare da karÉar dukkan wani Ęorafi da ya shafi harkar tantance ma'aikata."
0 Comments