By Muhammad Salisu, Kano
Yayin da Masu rajin yayata koken halin matsin rayuwa da Talakawan Nigeria ke ciki nan da farkon watan Ogustan wannan shekarar a duk fadin kasar ta hanyar zanga-zangar lumana, Wani Kwarren Lauya Barista Bulama Bukarti ya bada wasu Shawarwari guda biyar da ya kamata a kiyaye dasu.
Kwararran lauyan wanda ya wallafa shawarwari da ya bayar a shafin sa na Facebook a Larabar nan, ya bayyana cewa kiyayewa da shawarwarin zai taimaka matuka wajen cimma fa'idar da ake nema da yin zanga-zangar lumanar.
Cikin shawarwarin guda biyar, Barista Bulama Bukarti ya fa da shawartar masu niyyar gudanar da zanga-zangar lumanar kamar haka;
1. Ku tabbatar da cewa kun kafa tsayayyen shugabancin da zai ce a yi ayi, a bari a bari. Duk tafiyar ba shugabanci ba tafiya ba ce. Idan ku na tsoron kada a kama shugabanninku, ba sai kun bayyana sunayensu ba. Ku tabbatar da cewa abin magana (wato microphone) yana hannun mutum É—aya kuma kada a bar kowa yayi jawabi ko ya bada wani umarnin sai ya samu sahhalewan shugaba.
2. Ku tabbatar da cewa kun zayyana buƙatunku dalla-dalla. Misali: (1) Dawo da Tallafin Fetir (2) Dawo da Tallafin Naira, da sauransu. Kada ku ɗauko buƙatun da ba su da ma'auni ko kuma ba za a iya cin musu kusa-kusa ba kamar su (1) a dena cin hanci da rashawa ko kuma (2) stop bad governance. Waɗannan ba abubuwa ba ne za a iya samun su lokaci ɗaya kuma neman su zai iya kawar da hankalinku daga abubuwan da za a iya cin musu.
3. Ranar Zanga-Zanga, ku tabbatar kun bi doka da tsari. Ku ja kunne duk wanda ya fito cewa kada a taɓa dukiyar kowa kuma kada a cutar da kowa. Ƙone-ƙone da fashe-fashen kayan gwamnati da na jama'a ba zanga-zanga ba ne; hauka ne da ta'addanci. Duk wanda ya shigo cikinku da makami ko wani abin ɓarna, ku kama shi, ku miƙa wa jami'an tsaro.
4. Ba a iya yin zanga-zanga na tsawon lokaci babu hutu domin akwai bala'in gajiya kuma jama'a suna da buƙatar fita neman abinci ko makaranta. Saboda haka, kamata yayi ku ware kwana ɗaya ko biyu duk sati na zanga-zanga, sauran kwanaki kuma kowa ya tafi harkokinsa.
5. Da zarar kun samu abinda kuka fita nema, to ku kawo ƙarshen zanga-zanga. Kada ku yarda wani ya fito muku da sabbi buƙatu ya yaudare ku cewa a ci gaba. Misali: duk wanda ya ce muku kada ku bar zanga-zanga sai Shugaba Tinubu ya sauƙa to ɗan'adawa ne kawai kuma yaudarar ku ya ke.
Daga karshe kwararran lauyan, ya rufe shawarwarin da ya bayar ta hanyar tinasar da cewa, "Shugaba Tinubu shine zaɓeɓɓen Shugaban Najeriya kuma Kuɗin Tsarin Mulki ya ba shi dama ya yi mulki har ƙarshen wa'adinsa. Idan kuka ce sai ya sauƙa, to kun saɓa doka kuma ba ku nemi a zauna lafiya ba."
0 Comments