Header Ads Widget

An kafa kwamatin binciken asarar rayukan da aka samu yayin zanga-zangar lumana a Kano

Gov Abba Kabir Yusif


Daga Faruk Muhammad, Kano 

Gwamnatin Kano ta kafa kwamatin binciken asarar rayuka da dukiyoyi da suka faru lokacin Zanga-zangar lumana a Kano.
.....................................................
Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamatin bincike data daurawa alhakin zakulo ainin abinda ya faru a ranar farko da aka gudanar da Zanga-zangar lumana wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka da barnata kayayyakin gwamnati da satar dukiyoyin Al'umma na dinbin kudade.

Wannan na zuwa ne a dai lokacin da Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da Amnesty international suka ke matsa kira ga gwamnatin data yi bincike game da rahotannin munanan abubuwan da ke faruwa musamman na kisan rayukan jama'a wadan da ake zargin Jami'an tsaro da yi.

Yayin taron manema labarai a Litinin din nan, wanda ya gudana a fadar gwamnatin Kano, Maimagana da yawun Gwamnan Kano Sanusi Bature yace, gwamnati na cigaba da bibiyar halinda da ake ciki a fadin jihar.

Mai magana da yawun gwamnan yace, a yanzu haka an gwamnatin karkashin ma'aikatar shari'a ta jiha ta fara gabatar da wadanda aka kama bisa tuhumar tada zaune tsaye da aika abubuwan da suka faru marasa dadi wanda yawan su ya haura 600 a yayin gudanar da Zanga-zangar lumana a Alhamis din data gabata.

Haka kuma, gwamnatin jiha ta kafa kwamati na musamman domin fara tantance yaran da za'a kaisu cibiyar horarda yaran da suka samu kansu a matsalar shaye-share dake Kiru wadda gwamnatin jihar ta samar domin kula dasu.

Newskeeper ta rawaito cewa, a dai dai lokacin da aka fara samun lafawar tarzomar data barke a jihar Kano yayin fara zanga-zangar lumanar da ke gudana a fadin Nigeria kwanaki 5 da suka gabata, yanzu haka gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana zirga-zirgar jama'a ta awanni 24 data sanar, inda a yanzu gwamnatin ta sassauta dokar domin jama'a su futo harkokin su daga karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana.

Post a Comment

0 Comments