By Muhammad Salisu
Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki nauyin gasar karatun Alkur’ani ta kasa, ga yara marayu na jihohi 28 na Najeriya kadai.
Gidauniyar Aytam ta kasa da kasa ce ta shirya taron domin karfafawa da tallafawa marayu wajen neman ilimi a matsayin ginshikin wajen gudanar da rayuwa cikin al’umma.
Gasar dai, ta dauki tsawon makonni biyu ana yinta da nufin bunkasa ilimin addini da tarbiyyar tarbiyya a tsakanin matasa.
Da yake jawabi yayin rufe taron a ranar Lahadin nan, gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya jaddada muhimmancin ilimi wajen samun tarbiyya da samun nasara a rayuwa.
Gwamnan wanda ya yi yabon tare da bawa wadanda suka shirya Musabaqar tabbacin cigaba da bada goyon baya, ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa Hukumar Ilimin Tsangaya, domin inganta tsarin karatun Alqur’ani da kuma magance barace-baracen yara kanana.
Tun da farko babban jami’in kula da gasar ta kasa Dr. Mubarak Ahmad ya bayyana cewa, an shirya gasar ne da nufin zaburar da yara marayu don neman ilimi da kuma zama nagartattun al’umma.
Dr. Ahmad ya nuna godiya ga gwamnatin jihar Jigawa bisa goyon bayan da ba a taba yin irinsa ba wajen samun nasarar taron.
Ya ce, uwargidan gwamnan, Hajiya Hadiza Umar Namadi ce ta dauki nauyin gudanar da gasar.
Newskeeper ta rawaito cewa, an kammala taron ne da bayar da kyautuka ga wadanda suka yi nasara cikin daliban.
0 Comments