By Faruk Muhammad, Kano
Gwamna Kano Abba Kabir Yusif ya bayyana janye dokar hana fita baki daya daga wannan Rana ta Litinin.
Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai yayin ziyarar da yakai babbar kotun Jihar Kano a Litinin din nan, don ganin irin ta'adin da ya afkuwar yayin zanga-zangar lumana a Kano wadda ta gudana a duk fadin Jihar.
Abba Kabir yace gwamnati ta dauki matakin ne bayan gamsuwa da tayi game da cigaban da aka samu ta bangaren tsaro bayan tatttaunawarsu da Jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Newskeeper ta rawaito cewa, gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana zirga-zirgar ne a fadin jihar sakamakon samun tarzoma a wasu sassa tin ranar da kafa fara zanga-zangar lumana data gudana a duk jihohin Nigeria, inda daga bisani aka sassauta dokar kullen har sau biyu kafin daga bisani a yammacin Litinin din nan a dage dokar gaba daya.
0 Comments