By Muhammad Salisu, Kano
Gwamnatin Jihar Kano a karo na biyu ta sake sassauta dokar kulle data saka ta yadda a yanzu jama'a zasu dinga futa daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Gabanin wannan lokacin dai gwamnatin ta fara sassauta dokar kullen data fara sanarwa ta awanni 24 sakamakon hatsaniyar data biyo bayan Zanga-zangar lumana a Kano, inda ta rage lokacin dokar daga 8 zuwa 2 na rana, bayan da a karo na biyu aka sake sassauta dokar bisa la'akari da fara samun komawar lamura yadda suke a sassan Jihar.
Kwamashi nan ya sanda na jihar, Salaman Dogo ne ya sanarda hakan ga manema labaru jim kadan bayan kammala taron Majalisar tsaro ta jiha da ya gudana a Talatar nan wanda Gwamna Abba Kabir Yusif ya jagotanta a gidan gwamnatin Kano.
Kwamashinan Yan sandan yace Majalisar tayi nazari sosai game da halinda ake ciki a fadin jihar biyo bayan yamutsin da ya faru a jihar lokacin fara zanga-zangar lumanar dake gudana a sassan Nigeria.
Yace, Gwamnati da hadakar Jami'an tsaro za su cigaba da bibiyar yanayin tsaro domin yin abinda ya kamata a kowanne lokaci domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da cigaban al'amuran yau da kullun a fadin jihar Kano.
Newskeeper ta rawaito cewa, taron Majalisar tsaron ta jiha wanda ya dauki tsahon sama da awanni biyu, ya samu halartar Shugabannin dukkanin hukumimin tsaro dake Jihar Kano.
0 Comments