By Salisu K Ismail, Kano
Majalisar zartarwa ta Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin sake mayar da Jami'ar Ilimi ta Sa'adatu Rimi zuwa matsayin ta na Kwalejin ilimi kamar yadda take ada.
A cikin watan Fabrairu na shekarar 2023 ne Gwamnatin Kano, karkashin jagorancin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta daga likkafar Kwalejin zuwa matsayin Jami'a bayan samun sahalewar Hukumar kula da Jami'o'i ta kasa.
Kwalejin wadda ke cikin tsaffin cibiyoyin ilimi da suka yi shura wajen samar da gogaggun Malamai a Arewacin Nigeria an samar da ita ne cikin shekarar 1982 kimanin shekaru 42 da suka shude a lokacin tsohon Gwamnan Kano Marigayi Muhammad Abubakar Rimi.
Majalisar zartarwar gwambatin Kano a zamanta na 18 da ya gudana a Larabar nan, ta amince da sauya jami’ar ilimin ta Sa’adatu Rimi zuwa matsayin ta nada wato 'Sa'adatu Rimi College of Education' Amma kuma za ta ci gaba da zama cibiyar bayar da takardar shahadar digiri.
Cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Kanon ta futar ta hannun Kwamishinan Yada labarai Baba Halilu Dantiye yace, "Daukar matakin ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, tare da shawarar wani kwamiti mai karfi da gwamnatin jihar ta nada domin duba matsayin jami’ar tare da tsara yadda za a inganta karatun ta."
Kwamishinan Yada labarai Baba Dantiye ya kara da cewa, "Binciken da kwamitin ya yi ya nuna akwai damuwa daga bangaren ilimi dana gudanarwa da kuma sauran masu ruwa da tsaki dangane da illar da ke tattare da sauya zubin Kwalejin zuwa Jami'a."
Yace matsalolin da kwamitin ya hango nan gaba sun hada da kasadar rasa kwararrun malamai, rikice-rikice masu alaka da albashi, da kalubalen gudanar da mulki da ka iya kawo cikas ga gudanar da ayyukan Kwalejin.
Kakakin Gwamnatin Kano Baba Dantiye ya Kuma tabbatar da cewa, Akwai Kwalejojin Ilimi da dama a fadin kasar nan da suka samu nasarar gudanar da ayyukansu ba tare da rikidewa zuwa Jami'a ba, kuma sun ci gaba da bada shahadar Digiri a karkashin tsarin “Dual Mode” da hukumar NCE ta bullo da shi.
Jaridar Newskeeper ta rawaito Kwamishinan na cewa, wannan sauyin ba zai yi wata illa ga dalibai ba, domin wadanda ke karatun digiri na farko a Kwalejin za su ci gaba da karatunsu. Yayin da za a adana takardar shaidar Jami'ar cikin aminci don amfani nan gaba.
0 Comments