By Salisu K Ismail
A wani yanayi da ba kasafai aka saba ganin hakan na faruwa ga Shugabanni a fadin Nigeria ba, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusif ya nuna alhini da kulawa, inda ya tsayar da ayarinsa a daji domin tabbatar da tsaro da kulawa ga Tawagar ‘yan jarida da motarsu ta lalace, yayin wata ziyarar duba ayyukan da Gwamnan jagoranta a yankin kananan hukumomin Albasu da Garko.
Wannan lamarin ya faru ne yayin da Gwamnan ya baro karamar hukumar Albasu kan hanyarsa ta zuwa garin Garko domin cigaba da duba wasu ayyukan a yammacin ranar Lahadin nan da ta gabata, duk da cewa ana cikin yanayin fargaba da tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin Nigeria.
Inda ba tare da bata lokaci ba, Gwamna Yusuf ya umarci ayarin motocinsa da su tsaya, domin taimakawa da kuma fifita kulawa da lafiyar Yanjaridun da ke cikin motar data lalacen fiye da tarun ayyukan da ke gabansa na wannan ziyara da aka tsara.
Matakin da Gwamnan ya dauka na nuna rashin son kai ya baiwa mutane da yawa mamaki, duba da irin matsalolin da tabarbarewar tsaro ke cigaba da haifarwa a sassa daban daban na kasar.
An rawaito cewa, tsayawar ayarin motocin na kusan mintina 25 kafin a kammala gyaran motar data samu matsalar a jeji ya haifar da cikas na wani dan lokaci a rangadin da gwamnan ya shirya yi.
Har ila yau, an hangi Gwamna Abba Yusif na zaune cikin yanayi da nuna damuwa da sanya idanu, cikin yanayi na hakuri da karfafa gwiwa ga wadanda ke cikin ayarin nasa, har sai da ya tabbatar an sama musu da mafuta wajen gyara motar ta su.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Yanjaridun dake aikin dauko rahoto daga Gidan Gwamnatin Kano Comrade Adamu Dabo ya ce, "Wannan ba shi ne karon farko ba, da Gwamnan ya nuna irin wannan alhinin jagoranci bisa misali."
“Lamarin ya faru ne da daya daga cikin karin motar mu (Hilux) mai dauke da masu daukar hoto da masu kula da sauti da sauran ma’aikatan kafafen sada zumunta wanda tayar motar su ta lalace, amma Masha Allah, daga karshe dai an gyara ta yayin da ma’aikatan da ke cikin motar suka ci gaba da aikinsu," a cewar sa.
Ya kara da cewa, "Mituna kusan 25 da Gwamnan yayi wajen Jira har sai da aka gyara motar ya nuna matukar damuwarsa kan walwala da tsaron mutanen da ke aiki karkashinsa."
Wannan lamari dai ya janyo yabo ga Gwamna Yusuf, wanda ya nuna cewa tausayi da mutuntaka na iya yin galaba ko da a lokuta masu wahala.
Wani dan jarida a ayarin gwamnan Abdullahi Alkasim ya yi tsokaci cewa, “A yankin da ke fama da rashin tsaro da fargaba, alhinin da gwamnan ya nuna ya tunatar da mu cewa, shugabanci ba wai aiyuka da aiwatar da manufofin gwamnati ba ne bane kawai, ya kunshi nunawa mutane kulawa da tausayi cikin abinda ya shafe su.
Jaridar Newskeeper ta rawaito cewa, An hangi masu hucewa a dai-dai inda lamarin ya faru, suna taruwa kadan da kadan dan kallon abinda ke faruwa cikin mamakin ganin yadda Gwamna sukutum ya ja ya tsaya cak domin nemarwa Yan ayarin nasa mafuta sabanin abinda aka saba gani ga wasu Shugabannin.
0 Comments