Daga Rabiu Sanusi
Dan takarar karamar hukumar Nasarawa dake jihar Kano karkashin Jam'iyyar NNPP dake jihar Kano Hon. Yusuf Imam da akafi sani da ''OGAN BOYE'' ya bayyana kudurin sa na ganin maido da martabar karamar hukumar da yake takara kan turbar data dace.
Ambassada Yusuf Imam ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da suke taron kaddamar da takara da shirin fara gudanar da yakin neman zabe a fadin mazabu 11 dake fadin karamar hukumar.
Ogan Boye ya tabbatar dacewa wannan takara da zasuyi ba dan Amfanin Kansu bane burin su yadda zasu taimaki Al'ummar karamar hukumar su mai albarka.
''In sha Allahu nida mataimaki na Hon Dahiru Aro dakata da Sakataren wannan tafiya Hon Mai Kaba da sauran Jagororin mu zamuyi bakin kokarin mu dan mu samu yadda zamu taimaki jama'ar mu.
Dan takarar ya kuma bayyana matukar godiyar sa wajen yadda uwar Jam'iyyar NNPP ta jihar Kano ta basu damar tsayawa takara a wannan karamar hukuma.
''Kazalika muna godiya ga mai girma gwamna Abban Kanawa bisa bani dama da yayi dan zama daya daga cikin manyan masu bashi shawara a wannan gwamnati,fatan mu shida Jagoran mu Dr Rabiu Musa Kwankwaso Allah yaci gaba da Dafa Masu.
''Zamu fara gudanar da zagayen kamfen neman goyon bayan jama'ar mu daga ranar Alhamis din nan,inda zamu dauki kwanaki hudu kafin mu kammala a mazabu 11 na wannan kananan hukumomi.
Ambassadan ya kuma bukaci magoya bayan shi dasu kara basu goyon baya da Addu'a dan ganin sun samu nasarori a wannan zabe da za'a gudanar.
Shima a nasa jawabin daya daga cikin Jagororin NNPP naa Nasarawa Alhaji Yahuza Yankaba yace bayyana cewa kowane dan takara ya karbi takardar shi tare da zuwa mazabar shi dan kafa kwamitin yakin neman zaben daaa za'a gabatar.
Yahuza Yankaba ya kuma kara mika godiyar mu ka masoya da magoya bayan mu,bisa irin dafifin da suka yi wajen zuwa wannan taro.
Jagoran ya kuma mika sakon babban Jagoran NNPP na wannan Karamar hukuma da bai samu damar zuwa ba,bisa wasu dalilai watau Hon Mustapha Maisikeli dafatan alkhairi ga dukkan mahalarta taron.
Wakilin mu ya ruwaito cewa karamar hukumar Nasarawa dai a jihar Kano na daya daga cikin manyan kananan hukumomi 44 masu daraja da take da mazabu 11.
Haka kuma a lokacin taron shugabannin taron sun gabatar da wasu kwamitocin da zasu lura da yadda yakin neman zaben har zuwa samun nasara cin zabe.
Kwamitocin aun hadar da kwamitin bai daya da Hon Dan Sani Hotoro watau daraktan yakin neman zaben zai jagoran ta,sai kwamitin hada kan Mata.
Sauran sun hada da kwamitin hadin kan matasa,kwamitin Tsaro,kwamitin tsare-tsare,Kwamitin Kudi sai kuma kwamitin samun nasarar cin zabe
0 Comments