By Aisha Saleh
Ana fargabar sace wasu Kananan Yara da yawan su ya kai kusan 20 a Maradun ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da safiyar Lahadin nan, a lokacin da yaran suka je itacen girki a kusa da babban asibitin garin na Maradin.
Wani dan garin na Maradun da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa da da manema labarai cewa, maharan sun je da muggan makamai a bisa babura a lokacin da suka sace yaran.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta hannun kakakinta, DSP Yazid Abubakar ta ce za ta bincika domin kara tabbatar da lamarin ga manema labarai.
0 Comments