By Aisha Saleh
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kara kudin wutan lantarki a watanni masu zuwa, saboda bukatar samar da farashin bai daya don jawo hankulan kamfanoni masu zaman dake bukatar zuba hannunun jari a harkar wutar lantarki.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin makamashi Olu Verheijen ne ya bayyana haka a wajen taron shugabannin kasashen Afirka kan makamashi da aka yi a birnin Dar-es-Salaam na kasar Tanzaniya, inda Najeriya ta gabatar da wani shiri na dala biliyan 32 na fadada hanyoyin wutar lantarki nan da shekarar 2030.
Verheijen ya jaddada cewa yayin da za a daidaita jadawalin kuÉin fito don nuna ainihin farashi, gwamnati na da niyyar rage tasirin masu karamin karfi ta hanyar tallafin da aka yi niyya.
Najeriya ta fitar da wutar lantarkin N181.62bn cikin watanni 9.
0 Comments