By Aisha Saleh
Kirkiro da Abuja a matsayin babban birnin tarayyar Najeriya, ko me ye manufa kuma ko a wanne lokaci wannan kuduri ya cika.
Wane ne ya kirkiro Abujan Kuma lokacin wanne Shugaban kasa aka tabbatar da kudurin ? Jaridar NEWSKEEPER HAUSA ta yi nazari game a wannan batu.
A wannan rana mai kamar ta yau 3 Ga Watan Fabrairu 1976, Janar Murtala Ramat Muhammed (1938-1976) ya ayyana Abuja a matsayin sabon babban birnin tarayya.
A ranar 12 ga watan Disambar 1991, Shugaban Kasa Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya Dauke babban birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja saboda karuwar jama'ar Legas wanda ya sanya birnin ya cika da cunkoson jama'a da kuma yanayin da ake ciki.
Kungiyar International Planning Associates (IPA) ce ta samar da babban tsarin na Abuja babban birnin tarayya (FCT) da hadin gwiwar wasu kamfanoni uku na Amurka: Kamfanin Bincike da Tsare-tsare; Wallace, McHarg, Roberts da Todd; da Archisystems, wani yanki na Hughes Organization.
Yankin yana arewa da mahadar kogin Neja da kogin Benue. Tana iyaka da jihohin Neja zuwa yamma da Arewa, da Kaduna a arewa maso gabas, Nasarawa a gabas maso kudu, da Kogi a kudu maso yamma.
Birnin a yanzu haka yana da Kusan mutane miliyan 2.5 wadanda suke zaune a birnin. An gama gina sassan farko na birnin a karshen shekarun 1980.
0 Comments