By Aisha Saleh
Ƙungiyar Transparency Internaltional ta fitar da rahoto na ayyukan cin hanci da rashawa a duniya cikin shekara ta 2024, wato Corruption Perception Index.
Rahoton ya yi nazari ne kan ƙasashe 180 bisa la'akari da hujjojin masana da kuma ƴan kasuwa kan matsalar rashawa na kowace ƙasa.
Haka nan rahoton ya dogara da majiyoyi 13 masu zaman kansu domin ɗora ƙasashen kan mizani daga sifili zuwa 100; sifili na nufin matsalar rashawa ta yi muni sosai yayin da 100 ke nufin babu matsalar baki ɗaya.
Rahoton ya ƙara fito da bambancin da ke tsakanin ƙasashen da ke bin tafarkin dimokuraɗiyya da kuma waɗanda ke bin tsari na kama-karya.
Lamarin ya nuna cewa ƙasashen da ke bin tafarkin dimokuradiyya sau da ƙafa na da matsakaicin maki da ya kai 73, waɗanda ke bin tsarin dimokuraɗiyya mai cike da kurakurai kuma na da matakaicin maki 47 sai kuma ƙasashen da ba su bin tafarkin dimokuraɗiyya waɗanda ke da matsakaicin maki 33.
Ƙasashen da suke da sauƙin cin hanci a duniya
Mafi yawan ƙasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne.
Bakwai daga cikin ƙasashen 10 na farko, waɗanda ba su da matsalar Rasha duk a yankin Tarayyar ta Turai suke.
Ƙasar da ta fi kowace a duniya samun maki a ɓangaren yaƙi da rashawa ita ce Denmark, wadda take da maki 90.
Sai kuma Finland mai maki 88, ta uku kuma ita ce Singapore, wadda ke a kudu maso gabashin nahiyar Asiya.
Ga yadda ƙasashen 10 na farko suka kasance:
1. Denmark - Maki 90
2. Finland - Maki 88
3. Singapore - Maki 84
4. New Zealand - Maki 83
5. Luxembourg - Maki 81
6. Norway - Maki 81
7. Swtizerland - Maki 81
8. Sweden - Maki 80
9. Netherlands - Maki 78
10. Austria - Maki 77
Sai dai rahoton na Tranparency International ya ce duk da cewa ƙasashen Turai su ne suka fi samun yabo a rahoton, to amma makin da suke samu ya ragu cikin shekara biyu a jere.
Rahoton ya ce wasu shugabannin ƙasashen na Turai sun mayar da hankali wajen "abin da zai daɗaɗa wa harkar kasuwanci kawai a maimakon abubuwan da za su inganta rayuwar al'umma".
Ƙasashen da ke kurar-baya
Rahoton ya nuna cewa akasarin ƙasashen da ke ƙasan jadawalin suna a nahiyar Afirka ne, inda nahiyar ke da ƙasashe shida cikin 10 da suka samu maki mafi ƙaranci.
Sauran ƙasashen sun fito ne daga nahiyar Amurka ta kudu sai kuma Gabas ta takiya.
Sudan ta Kudu da Somaliya su ne ƙasashen da ke ƙasar tebur, inda Sudan ta Kudu ke da maki 8 kacal yayin da Somaliya ke da maki 9.
170. Sudan - Maki 15
172. Nicaragua - Maki 14
173. Equatorial Guinea - Maki 13
173. Eritriya - Maki 13
173. Libya - Maki 13
173.Yemen - Maki 13
177. Syriya - Maki 12
178. Venezuela - Maki 10
179. Somaliya - Maki 9
180. Sudan ta Kudu - Maki 8
Rahoton ya ce nahiyar Afirka, kudu da hamadar sahara ce ta samu maki mafi ƙaranci. Hakan ya faru ne sanadiyyar rikice-rikice masu alaƙa da sauyin yanayi waɗanda ke tarnaƙi ga ci gaban yankin.
Sai dai rahoton ya ce bunƙasar yaƙi da rashawa a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Amurka wani abu ne na farin ciki, sai dai wannan ne karo na farko da aka samu haka a cikin shekara 10, kuma ci gaban da maki ɗaya ne kacal.
Mene ne matsayin Najeriya?
Najeriya na a matsayi na 140 inda ta samu maki 26, tare da wasu ƙasashen kamar Mexico da Iraqi da Kamaru.
0 Comments