By Aisha Saleh
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti da ma’aikatu don tabbatar da cikakkun bayanai na rajistar shaidar zama dan kasa domin shirye-shiryen saka hannun jari na gwamnatin tarayya.
Wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa ta shaida wa jaridar PUNCH a ranar Asabar din da ta gabata cewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana wa majalisar zartaswar gwamnatin tarayya a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025 kan ayyukan hukumar NIMC da ke karkashin sa.
Rahotanni sun bayyana cewa ministan ya tabbatar da cewa an cire NIN din wadanda aka cike ba tare da ka'ida ba a wani abin da akayi ikirarin aikin tsaftace bayanan shaidar zama dan kasa.
A ranar 13 ga Oktoba, 2022, hedkwatar tsaro da ke Abuja ta ce sojoji tare da rundunar ‘yan sandan Najeriya da jami’an hukumar shige da fice ta kasa sun cafke wasu jami’an hukumar NIMC guda biyu da ake zargin na jabu ne.
Daraktan yada labarai na tsaro na lokacin, Maj.-Gen. Musa Danmadami, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “An bayyana cewa wadanda ake zargin sun ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Gagamari da ke jamhuriyar Nijar ne domin yin rijistar wadanda ba yan Najeriya ba a sansanin yan gudun hijira.
“Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da na’urar rijistar lamba ta kasa, na’urar buga takaddu, injin laminating, na’urar bin diddigin kwamfuta da injin janareta da dai sauransu.”
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an na jabu suna neman wadanda ba ‘yan Najeriya ba ne, musamman daga kasashe makwabta irin su Jamhuriyar Nijar, kan suyi NIN na Najeriya.
Bincike ya nuna cewa irin wannan rajistar na bogi ya faru ne a cikin al’ummomin kan iyaka, lamarin da ke kara ta’azzara hadarin shigowa ba tare da izini ba wajen samun takardar shaidar zama dan Najeriya.
NIMC na shigar da ‘yan kasa da masu ziyara da masu zama, tana ba su NIN na musamman.
Lambobi 11 ana daura sune ta samun bayanan halittu na mutum da bayanan alƙaluma, domin samar da lambobin zama dan kasa ga duk wani dan kasa.
"Ministan cikin gida ya ce NIMC tana aikin tattara bayanan ne saboda sun gano sama da mutane 6,000 daga Jamhuriyar Nijar da suka samu NIN. Amma an goge su daga rumbun adana bayanai.
Ma'aikatar jin kai tana buƙatar bayanan takardun shaidar zama dan kasa domin yin aiyukanta. Hakanan, ma'aikatar ilimi tana buƙatar waɗannan bayanan domin bada lamunin ɗalibai.
0 Comments