By Aisha Saleh
Ministan sufuri a Nijar, Kanal Manjo Salissou Mahaman Salissou ya ce Ĉawancen Ĉasashen Sahel, da ya haÉa Burkina Faso da Nijar da Mali, na shirin kafa kamfanin sufurin jirgin sama domin Ĉarfafa haÉin gwiwar sabuwar Ĉungiyar, kamar yadda kafar yaÉa labarai ta ActuNiger ta ruwaito.
Salissou ya ce kafa kamfanin sufurin jirgin saman na AES abu ne mai muhimmanci da za su mayar da hankali a kai, kuma nan ba da jimawa ba za su samar da kamfanin mai launin Ĉasashen, wanda zai haÉa manyan biranensu da ma wasu wuraren.
Ministan ya kuma ce shugabannin mulkin soji a Niamey sun umurci hukumomin da ke kula da fannin sufurin jiragen sama su 'sassauta wasu dokoki'' domin a gaggauta samar da kamfanin jirgin sama na yankin da ma na Ĉasar.
A baya Ĉasashen Ĉawancen na AES waÉanda ke ĈarĈashin mulkin soji sun Ĉaddamar da fasfo Éin bai-Éaya, sun kuma sanar da kafa dakarun haÉin gwiwa domin daĈile Ĉungiyoyin Ĉ´an bindiga da ke addabar yankin bayan ficewar su daga Ĉungiyar ECOWAS.
0 Comments