By Aisha Saleh
A ranar 8 Ga Watan Fabrairu a shekarar 2013 wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar ta’adda ta Boko Haram ne suka bindige akalla mata tara da suke gudanar da aikin rigakafin cutar shan inna a Kano...
Nan take kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Idris ya bayar da umarnin cafke wasu ‘yan jarida uku na gidan rediyo bisa zarginsu da tunzurawa wajen kashe-kashen. 'Yan sanda sun yi ikirarin cewa sunyi wasu kalamai a Radio.
Yan bindiga a kan babura sun harbe wasu ma’aikatan lafiya 9 da ke aikin allurar rigakafin cutar shan inna a wasu hare-hare guda biyu da aka kai a birnin Kano da ke arewacin Najeriya a ranar Juma’a, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar Boko Haram, wadda ta yi Allah wadai da amfani da Rigakafin magungunan kasashen yamma, ana zargin ta da kai hare-hare kan jami’an tsaro.
Wasu jiga-jigan Musulmi a Kano sun fito fili suna adawa da allurar rigakafin cutar shan inna, su na masu cewa makirci ne da ake kullawa yaran Musulmi. Game da wani gangamin rigakafin da aka yi a yankin ne ya haddasa hare-haren.
Hare-haren sun shafi kokarin da kungiyoyin lafiya ta duniya ke yi na kawar da cutar shan'inna ta hanyar kare kananan Yara musamman Yan kasa da shekaru 5 da haihuwa daga kamuwa da cutar.
0 Comments