Header Ads Widget

Shekaru 4 Da Sace Dalibai Mata A Jangeben Jihar Zamfara | Newskeeper Hausa

Shekaru 4 Da Sace Dalibai Mata A Jangeben Jihar Zamfara.


By Aisha Saleh 

A Rana mai Kamar Ta Yau 26 Ga Watan Fabrairu 2021 ‘Yan bindiga sun sace dalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 17 a jihar Zamfara da Arewa maso yammacin Najeriya.

Satar da aka yi a Zamfara (ko garkuwa a Jangebe) shi ne sace dalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 17 a wani samame da ‘yan bindiga suka kai ranar 26 ga Fabrairu 2021. 

A lokacin, an yi garkuwa da mutanen ne a makarantar kimiyyar ’yan mata ta gwamnati, makarantar kwana da ke Jangebe a jihar Zamfara a Najeriya.

Dalibai mata kusan 300 wasu 'yan bindiga suka sace daga wata makarantar sakandare ta kwana da ke jihar Zamfara. 

Rahotanni sun bayyana cewa, yayin faruwar lamarin wanda wasu 'yan bindiga suka sace yan' matan a daren Alhamis din 26 ga watan Fabrairu 2021, lamarin ya jefa al'ummar garin musamman iyayen yaran cikin rudani. 

Wannna kusan shi ne karan farko da aka shiga makatarantar kwana ta mata, aka kwashi dalibai a shiyyar arewa maso yamma, lamarin da ya tayar da hankulan al'umma ta la'akari da yadda lamarin ya auku a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ke cewa tana sasantawa da 'yan bindiga.

Sace wadannan dalibai na zuwa ne, a  lokacin da gwamnonin arewacin kasar ke taro a jihar Kaduna da zummar magance matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Najeriya na daga cikin wuraren da ake yawan sace mutane a duniya. 

Wata kiddiga ta nuna cewa zuwa yanzu akwai sama da mutane 3,000 aka yi garkuwa da su a Najeriya tun daga farkon shekarar 202.

Post a Comment

0 Comments