Header Ads Widget

Yaushe Aka Kaiwa Gidan Fela Hari ? | Newskeeper Hausa

Fela Anikulapo

By Aisha Saleh 

A rana Mai Kamar Ta Yau 18 ga Fabrairu, 1977, Gwamnatin Najeriya Ta Olusegun Obasanjo ta Tura wata bataliyar Sojoji Guda 1000 (kamar za a kamo shekau ko wani turji) zuwa gidan Fela Anikulapo Kuti wanda aka fi sani da Jamhuriyar Kalakuta domin kamo Mawakin.

A lokacin da Sojoji suka isa Gidan sunyi arangama da Mutanen gidan da sukayi ta jifan Sojojin da duwatsu da kwalabe, sojojin sun bankawa gidan wuta tare da kama mawakin bayan sun lakada masa dukan tsiya, yayin da kuma suka wurgo mahaifiyarsa mai shekaru 78 mai suna Olufunmilayo Ransome- Kuti ta tagar bene, wacce kuma fitacciyar mai fafutukar kare hakkin mata ce, ta Karye a kafa da kuma samun munanan raunuka.

Samamen da aka kai da sanyin safiyar ranar 18 ga watan Fabrairu ya zo da mamaki domin sama da sojoji dubu ne suka mamaye Gidan da sunan kame fitaccen Mawakin na Afrobeat da ke ajiye yara mata masu karancin shekaru a gidansa.

A karshe ta Mahaifiyar tasa ta rasu bayan Makonni 8. Shekara Guda Bayan lamarin ya sa marigayi Fela ya jagoranci zanga-zangar zuwa Barikin Dodan, wadda ita ce fadar mulki a lokacin, kuma ya jefar da akwatin gawar ta a kofar Barikin bayan da sojoji suka hana shi shiga. Makonni da faruwar lamarin, ya fitar da wakoki guda biyu, 1, Akwatin gawar shugaban kasa, 2, sojan da ba a sani ba. Wakokin Sunyi magana ne a kan lamarin da ya faru.

Post a Comment

0 Comments