By Aisha Saleh
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin da take da shi na cin tarar kudi mai yawan gaske ga mamallaka gidajen da suka gaza saka mutane a cikin a wani mataki na rage karancin muhalli a kasar nan.
Ministan gidaje da raya birane na kasa Arc.Ahmed Musa Dangiwa ne ya tabbatar da hakan yayin wata ganawa da manema labaru a karshen makon jiya, inda ya ce duk mai gidan da ya gaza saka ’yan haya ko kuma ya sayarwa masu bukata to kuwa zai fuskanci hukunci ta hanyar biyan haraji mai yawa a kan gidajen.
Ministan ya ce, babu dalilin da zai sanya a rinka kukan karancin gidaje a kasar nan, musamman ma a manyan birane alhalin kuwa ga gidaje da dama da attajirai da ’yan kasuwa suka gina, amma kuma sun gaza sayarwa ko kuma bayarwa haya.
Ko da yake ministan ya ce, gwamnati ba za ta tilastawa kowa ba kan ya sayar ko kuma ya bayar da hayar gidansa, amma kuma za a sanya masa haraji mai yawa da zai rinka biyan gwamnati a kan duk wani gida da babu mutane a cikinsa.
Arc. Ahmed Musa Dangiwa ya ci gaba da cewa, gwamnati ta tsara cewa duk gidan da aka kiyasta kudinsa zai kai naira miliyan 5 kuma aka bar shi ba tare da kowa a cikin sa ba, gwamnati za ta rinka karbar harajin naira miliyan 3 a duk shekara a matsayin harajin kasa.
Ministan ya ce, domin tabbatar da nasarar wannan shiri, tuni gwamnati ta fara aikin kidaya na irin wadannan gidaje a duk fadin kasar wanda kuma ake daf da kammalawa, kuma masana shari’a na nazartar hanyoyin da za a bi a aiwatar da wannan manufa ta gwamnati domin tabbatar da ganin ba a shiga hakkin mallakar kaddarori ba.
0 Comments