By Salisu K Ismail
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji/Kiru, Rt Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, PhD, a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023, ya shirya taro na musamman wanda ya haÉ—a sama da mutum 10,000 domin yin addu’o’i a garinsa na Kofa da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano.
ÆŠan majalisar mai hawa huÉ—u ya shirya taron ne domin ya gode wa Allah saboda nasarar da ya samu a Kotun Sauraron Ƙararrakin ZaÉ“e da ta ÆŠaukaka Ƙara da ke Abuja a kwanakin baya, da kuma raba wasu kayan tallafi ga ’yan mazabarsa.
A yayin kasaitaccen taron dai, an bayar da tallafi ga ’yan mazabar su 10,000 maza da mata. Bugu da Æ™ari, an ba mutanen tallafin kuÉ—i da kayan sanaa da motoci da kayan abinci da sutturu da kuma sauran kayan amfanin yau da kullum.
Kazalika, an yi addu’a ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin neman Allah Ya ba shi nasara a Kotun ÆŠaukaka Ƙara da ta Ƙoli, da sauran ’yan majalisar Kano na NNPP da suka yi nasara a kotu, da ma fatan nasara ga waÉ—anda ba a kai ga yanke nasu hukuncin ba. Sannan an yi wa jagoran ÆŠariÆ™ar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, addu’ar neman Allah Ya ja kwanan sa, Ya Æ™ara masa lafiya da kuma biya masa bukatunsa.
0 Comments