Header Ads Widget

Masu sana'ar yin gurasa a Jihar Kano sun yi zanga zangar lumana a Jihar

Hoton masu zanga-zangar


By Salisu K Ismail

Masu sana'ar yin gurasa a Jihar Kano sun yi zanga zangar lumana a Jihar 

Shugabar kungiyar masu sana'ar gurasar ta Jihar Kano, Hajia Fatima Auwal ta ce, sun gudanar da zanga zangar ne domin jankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki kan tsadar fulawa da sauran kayan yin wannan sana'a.


Masu zanga zangar wadan da suka futo a yakin unguwannin Jakara da Sanka da Yalwa da kuma Cediyar Yan' gurasa a Safiyar Juma'ar nan sun ce, yawancin su marayu da zawarawa ne sun kuma bayyana mawuyacin halin da suke ciki saboda tsadar rayuwa ta yadda har ta kai matsayin da wasun su jarin su ya karye, wasun su bashi ya taru akan su wanda a yanzu haka suna can daure a gidan kurkuku. 

A cewar su, da yawa daga cikin su hatta abinda za su ci a gidajen su ya gagare su, inda suka ce yawancin ya'yan'su a yanzu haka an koro su gida daga makaratun da suke karatu saboda rashin abinda zasu biyawa yaran kudin makaranta.

Wani rukuni na masu zanga-zangar

Yayin zanga zangar, Shugabar kungiyar Fatima Auwal tayi kira da kakkarfar murya da shugabanni a duk matakai dasu dubi halin da suke ciki na tsada da tsananin rayuwa.

Gurasa dai na cikin futattun abincin al'adar mutanen Kano mafi saukin sarrafawa tun zamanin kaka da kakanni wadda kuma har kawo yanzu ake alfahari da ita a matsayin abincin Bahaushe mafi sauki. 

Hajia Fatima Auwal.

Jaridar Newskeeper Hausa, ta rawaito yadda masu sana'ar yin gurasar ke kukan cewa tsadar kudin filawa yasa sana'ar ta gagari da dama daga cikin su kasan cewar a yanzu haka kudin buhun ta ya haura N43,000 a kasuwannin birnin Kano. 

Post a Comment

0 Comments