By Salisu K Ismail
Mai taimakawa Gwamna kan harkokin Mawallafa Alhaji Tijjani Gandu ya ce Babu wani abu da mutum zai rasa a tafiyar Gwamnatin Kwankwasiyya karkashin mulkin Abba Kabir Yusuf ya same shi a wani wajen.
Mai taimakawa Gwamnan Tijjani Gandu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da Yanjaridun fadar gwamnati, a Kano.
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da batun wadan su daga cikin Mawallafa da Mawaka da aka somo tafiyar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwankwasiyya tare dasu amma a baya-bayan nan suka sauya sheka zuwa Jam'iyyar APC karkashin Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa Sanato Barau Jibril, Shahararran Mawakin Tijjani Gandu ya ce babu wani mutun daya san abinda yake wanda zai bar Gwamnatin Abba Kabir Yusif duba da dinbin hidimtawar da takewa jama'a.
Ya kara da cewa "Gwamnati irin ta Abba Yusif itace abar bi indai mutun burin cigaban jama'a be a ransa, Kuma babu abinda mutum ya rasa a tafiyar Abba Kabir wanda zai same shi a wajen wani ko a wata jam'iyyar daban."
Yace banbacin dake tsakanin irin gwambatin kwankwasiyya a bayyane yake karara, Kuma a yanzu haka ma batun
A cewar sa "Batun sauyin sheka a yanzu tsohon yayi ne, gwara ma masu sha'awar yi su canja tunani."
Shahararran Mawakin wanda kuma shine jagoran dukkannin Mawallafa a tafiyar siyasar Kwankwasiyya Alhaji Tijjani Gandu ya kuma ce ba laifi bane mutun ya yi fushi kuma ya bayyana laifin da akayi masa, saboda haka inada yakinin duk wadanda suka yi fushi idan suka huce zasu dawo.
Dangane da batun tintuba wajen godo kan dawowar wasu daga cikin Mawallafan da suka yadda tafiyar kwankwasiyya, Tijjani Gandu ya tabbatar da cewa akwai tintuba da wasu suke yi Kuma magana tayi nisa wajen dawo da wadanda wani dalili yasa suka tsalle zuwa wani wajen, Amma akwai kakkarfan tabbacin dawowar su zuwa cikin jam'iyyar NNPP nan bada jimawa ba.
"Tabbas ina goyan bayan wannan tuntuba da ake game da bibiyar wadan da suka bar tsarin tafiyar mu, Yana mai karawa da cewa, yin hakan abune mai kyau idan masoyin ka ya ce ka bata masa rai ka rarrashe shi."
"Tafiyar kwankwasiyya tafiya ce ta ra'ayi da sakai da sadaukarwa, dan haka duk wanda ya shige ta kaga ya fita da sunan an bata masa rai to, muna da yakinin idan ya huce zai dawo, wanda wannan shine abunda ya faru da wasu daga cikin mu," a cewar sa
Yace Gwamna Abba Kabir Yusuf mutun ne adali, mai tausayi da haba haba da Jama'a, wannan tasa wasu suke ganin kamar ya fiya sanyi, kuma daga irin kamun ludayinsa zuwa yanzu da yaddar Allah kwalliya zata biya kudin sabulu wajen sauke amanar da Al'ummar Jihar Kano suka daura masa.
Yace gwamnati na kokari sosai wajen inganta sana'o'in Mawallafa da Mawaka da Yan fim, dan haka ta gyara tare da farfado da makarantun da Gwamnatin kwankwasiyya ta samar da suka jibanci wannan layi tun a shekarar 2011 zuwa 2015.
"Yanzu haka an sake bude wadannan makarantu, domin a yanzu ma tuni har an futar da takardun neman iznin shiga makarantun, kuma mu ma Mawallafa Gwamnati ta bamu "forms" domin mutanen mu su samu karin horo a sana'ar su, bayan sun kammala horo za'a yaye su kuma Gwamnati zata tallafa musu da kayyakin da suke bukata na zamani dan cigaba da aiwatar da sana'ar su."
Haka kuma, Tijjani Gandu ya bayyana cewa nan gaba kadan, shirye shirye sun yi nisa domin shirya taron bita ta musamman ga Mawallafa da Yan fim da Mawaka.
A bangaren tallafawa Jama'a, Shararran Mawakin ya ce kamar yadda Gwamna ya kuduri aniyar tallafawa jama'a, "Nima na nayi alwashin taimakawa jama'a ta kamar yadda muka somo daga unguwar Gandun Albasa inda a yanzu haka koda a kwanan nan na raba akalla babura masu caji guda 6 kuma za a cigaba da bada wannan taimako na motoci da babura da duk abubuwan da suka kamata domin karfafa gwiwar Al'ummar Jihar Kano domin su sami tsayawa da kafafun su.
Daga karshe, Mai taimakawa Gwamnan kan harkokin Mawallafa da Mawaka Alhaji Tijjani Gandu ya yi kira ga daukacin magoya bayan jam'iyyar NNPP dasu futo kwansu-da-kwarkwatar su wajen zaben wadanda jam'iyyar ta tsayar a zaben kananan hukumomi Jihar Kano 44 da zai gudana ranar 26 ga wannan wata na Oktoba.
0 Comments