Daga Aisha Saleh
Laftanl Kanal Pascal da ake zargi da kitsa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Benin a ranar 7 ga watan Disamba shekarar 2025 ya nemi mafaka a Togo, in ji kasar Benin.
Tigri da masu goya masa baya sun kasa karbe ragamar mulkin kasar ne bayan da Najeriya ta shiga tsakani tare da goyon bayan Faransa.
Shugaban kasar Benin Talon ya sha alwashin hukunta wadanda suka aikata laifin.
Jami'an gwamnatin Benin biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa jami'in da ake zargin ya jagoranci juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Benin ya nemi mafaka a kasar Togo.
Takaddamar da ta kunno kai tsakanin kananan kasashen yammacin Afirkan biyu, akan Kanar Pascal Tigri da wanda suka mara masa baya wajen kitsa juyin mulkin, za ta iya zama silar kara samun rarrabuwar kawuna a fannin diflomasiyya a Afirka ta Yamma.
Sojojin sun kwace iko da gidan talabijin na kasar Benin a safiyar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ikirarin cewa sun hambarar da shugaban kasar wato Patrice Talon, amma dakarun kasar Benin da ke samun goyon baya daga Najeriya da hukumar leken asirin Faransa sun dakile yunkurin.
Sojojin sun bayyana Tigri a matsayin jagoran juyin mulkin. A baya dai ba a san inda ya samu mafaka ba.
Sai de har yanzu ma'aikatar harkokin wajen Togo ba ta amsa bukatar yin magana akan batun ba.
Daya daga cikin jami'an kasar ta Benin ya ce Tigri da wasu da ake zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulkin na boye a wata unguwa da ke Lome babban birnin Togo da ake kira Lome 2 a gidan tsohon shugaban kasar Faure Gnassingbe.
Jami'in ya ce "Idan har gwamnatin Togo ba ta mika su ga kasar Benin ba, hakan zai zama hujjar cewa Togo na da hannu a yunkurin juyin mulkin."
Wata sanarwa da hukumar leken asiri ta kasar Benin ta aikewa takwararta ta Togo ta ce wasu sojojin kasar guda hudu ne suka nemi mafaka a kasar ta Togo.
A ranar da aka yi yunkurin juyin mulkin, wani mai amfani da lambar wayar Togo ya tuntubi Tigri.
“Sashen mu na son neman goyon bayan ku wajen kamawa da kuma mika wadannan sojojin da suka tsere zuwa kasar ku daga Benin ta hanyar kwararrun ma’aikatan ku,” in ji sanarwar.
Shugaba Talon ya sha alwashin daukar tsatstsauran mataki akan wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadin da ta gabata Talon ya bayyana cewa "wannan ha'incin da cin amanar baza su tafi a banza ba, dole ne a hukunta wanda suka aikata wannan laifi".
Wani cikakken bayanin gwamnati na yadda yunkurin juyin mulkin ya gudana ya ce an samu hasarar rayuka a bangarorin biyu.
Kasar Benin de na shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu shekarar 2026, wanda ake sa ran zai kawo karshen wa'adin Talon.
0 Comments